Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Ranar Yaki Da Cutar Sida


Gwajin HIV/AIDS
Gwajin HIV/AIDS

Jamhuriyar Nijar ta bi sahun sauran takwarorin ta na duniya wajan tunawa da ranar yaki da cutar Sida.

Hukumomin mulkin sojan kasar sun bayyana wa duniya irin halin da a ke ciki a Nijer game da yakin da a keyi da wannan cutar kuma duk da ana samun galaba, hukumomin sun ce za su kara dagewa wajen kara waye kai da ma rage yaduwar cutar ta Sida.

Taken ranar ta yaki da cutar Sida ta bana, shine: hada kan al'umma don su jagoranci yaki da cutar Sida - jaddadawa ga masu dauke da cutar Sida; muhimancin shan magani.

Wannan shi ya sa hukumomin sojan kasar su ka yi anfani da wannan damar don bayyanawa 'yan Nijar inda a ka kwana game da yaki da ma hana yaduwar cutar a cikin al'umma.

Kanal Manjo Docter Garba Hakimi shine Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Nijar. Ya ce;

A nan Jamhuriyar Nijar, duk da yake 0.4% na al'umma ne suka kamu da cutar, daga cikin mutanen da shekaru suka kai daga 15 zuwa 49 a wajan mata masu zaman kanun su, abin ya kai kashi 9.6%, yayin da yake kashi 1% ga wadanda ke tsare a gidan wakafi, yayin da abin ya kai a wajan 'yan gudun hijira da bakin haure kashi 0.7 %, yayin a matasa ya kai 0.8% a karkashin wata kididiga ta 2019.

Ministan, yace daga bisani wadanda suka kamu da cutar a binciken shekara 2022, sun kai dubu 33 da dari 854, yayin da wadanda suka rasu, sun kai dari 8 da 14, yayin da dubu 1 da dari 513 ne suka kamu da cutar kuma, Nijar na kokari wajan dakile yaduwar cutar ta SIDA.

Suma Malaman asibiti ta bakin mai kula da sadarwa da ma hulda da jama'a, Assumane Abdulmumuni na Babbar assibitin Birni N'Konni sun yi anfani da wannan ranar domin yin kira ga jama'a da suyi hattara don kar su kamu da wannan cutar ta SIDA.

Saurari rahoton Harouna Mamme Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG