Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kai Kamfanin Yada Labaran Switzerland Kara Kan Labarin Tabar Wiwi


Gonar tabar wiwi
Gonar tabar wiwi

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi OCRTIS a Jamhuriyar Nijar ta shigar da kara a kotu bayan da wata jarida mai zaman kanta dake da ofishi a kasar Switzerland ta ruwaito wani labari dake cewa wani bangare na tabar wi-wi da aka kama a Nijar a watan Maris din da ya gabata ya koma wajen mai shi.

Tun a watan da ya gabata ne kamfanin yada labarai na Initiative Mondiale Contre la Criminalite Transnationale Organisee mai cibiya a birnin Geneva ya ruwaito cewa dilan da aka kama Tonne 17 na tabar wi-wi a hannun yaransa lokacin da suke kokarin ratsa Nijar a watan Maris din da ya gabata ya fanshi wani bangare na wannan haja.

Labarin da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta ce kazafi ne, mafari kenan hukumar ta garzaya kotu domin a bi mata kadi kamar yadda aka sanar da manema labarai ta hanyar wata rubutacciyar sanarwa mai dauke da sa hannun babban darektan OCRTIS Controleur Aboubacar Issaka Oumarou.

Da yake bayyana matsayinsa a game da wannan dambarwa shugaban kungiyar ADENA mai yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi Ganda Saley na ganin abin tamkar wani yunkurin katsewa ma’aikata hamzarin aiki ne.

Hukumar ta OCRTIS a ci gaban sanarwarta ta kudiri aniyar yada wannan kara zuwa sassan duniya ta hanyar Interpol don ganin masu hannu wajen rubuta wannan labari sun gurfana a gaban koliya.

A cewar Son Allah Dambaji na kwamitin yaki da safarar mutane matakin ya yi dai-dai muddin za a baiwa ‘yan kasa damar sanin yadda shari’ar za ta kaya.

Kafar labarai ta Initiative Mondiale Contre la criminalite Transnationale Organisee na daga cikin cibiyoyin da suka yi fice wajen bankado bayanan dake da nasaba da masu aikata miyagun ayyuka a duniya.

Sai dai ta hanyar karar da ta shigar hukumar OCRTIS ta kalubalance ta tazo da hujjojin da za su gaskanta zargin an karkata akalar wani bangare na tabar wuy wuy tonne 17 da aka fito da ita daga kasar Lebanon.

Kawo yanzu cibiyar ba ta da wani bayyanan wakili ko kuma ofishin wakilci a nan Nijar ballantana a ji martanin da za su mayar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Kai Kamfanin Yada Labaran Switzerland Kara Kan Labarin Tabar Wiwi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


XS
SM
MD
LG