Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: 'Yar Majalisar Dokoki Ta Bukaci Samar Da Dokar Hukunta Masu Yayata Batsa A Kafofin Sada Zumunta


Taron 'yan Majalissar Dokokin Nijer
Taron 'yan Majalissar Dokokin Nijer

Wata ‘yar majalissar dokokin kasa daga bangaren masu rinjaye a Jamhuriyar Nijar, ta shawarci takwarorinta ‘yan majalissa da ma hukumomi akan bukatar nazarin hanyoyin warware sarkakiyar dake tattare da dokokin kasar game da batun mu’amular mutane masu jinsi daya.

'Yar majalisar Nana Jubi Harouna Maty, ta bada wannan shawarar ne bayan da a farkon watan nan na oktoba mahukunta suka kama wasu ‘yan mata da ake yi wa kallon ‘yan madigo yayinda hukumomin shara’a ke cewa laifin yada bidiyon tsiraici a kafafen sada zumunta ne mafarin cafke su.

Hanyoyin da matasan ke bi wajen amfani da kafafen sada zumunta wani abu ne da tun dadewa shugabanin addinai ke jan hankulan iyaye akansu.

Taron 'yan Majalissar Dokokin Nijer
Taron 'yan Majalissar Dokokin Nijer

Tun a washegarin bayyanar wani bidiyon tsiraicin da ya karade kafafen sada zumunta ne jama’a daga sassan Nijer suka tuntubi ‘yar majalisar dokokin kasa Nana Jubi Harouna Maty akan wannan al’amari da ya saba wa tsarin zamantakewar al’ummar Nijer kamar yadda ta bayyana a taron manema labaran da ta kira.

Ta ce abun da ya faru a Maradi, abun ta da hankali ne saboda akasarin 'yan Nijar, masu bin addini ne yadda ya kamata.

Majalissar Dokokin Nijer
Majalissar Dokokin Nijer

Girman damuwar da ake ta nunawa bayan faruwar wannan al’amari ya sa ‘yar majalisar yanke shawarar gabatar da korafin ‘yan kasa a zauren majalisar don ganin an samar da dokar kare al’umma daga miyagun ayyukan da alamu ke nunin idan masu bakin fada aji ba su yi wani abu akai ba abin na iya samun gindin zama a sahun al’ummar kasar.

Hanyoyin da matasan ke bi wajen amfani da kafafen sada zumunta wani abu ne da tun da dadewa shugabanin addinai ke jan hankulan iyaye akansu.

A hirar ta da Muryar Amurka, Malama Sakina Maman daya daga cikin masu gabatar da wa’azin addinin islama ta ce duk wasu mata biyu ko maza biyu, ko mace ta ce ita na miji ne ko namiji ya ce shi mace ce, to lalle su yi hankali domin Allah zai hallaka su kamar yadda yayi wa wadanda suka zo kafin mu.

Haka shi ma Reveran Pasteur Sabo Batchiri na Majami’ar Assemblee de Dieu ke cewa wajibi ne a ci gaba da tunatarwa akan nauyin da ya rataya a wuyan shugabanni .

A farkon watan nan na Oktoba ne hukumomin shara’a suka kama wasu ‘yan mata 13 a Maradi wadanda da farko rahotanni suka ce ‘yan madigo ne da dubunsu ta cika bayan bayyanar wani bidiyon da suka nada sai dai a washegari alkali mai tuhuma yace da laifin yada bidiyon tsiraici ne ya kama su a maimakon laifin aikata mu’amula irinta masu jinsi 1 da ake ta yayatawa mafari kenan wasu ‘yan kasa ke ganin akwai bukatar warware wannan kulli.

Saurare rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG