Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer Da Bankin Duniya Sun Cimma Yarjejeniyar Bilion 185 Na Cfa Don Samar Da Wutar Lantarki


Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta cimma  yarjejeniya da bankin duniya akan wani shirin samar da wutar lantarki da hasken rana wanda aka yi lakanin Haske Project da nufin inganta harkokin jama’a a birane da kuma karkara.

Kimanin billion 185 na cfa ne bankin duniya ya yi alkawalin bayarwa a karakshin wannan yarjejeniya da nufin ba gwamnatin Nijer damar cimma gurinta na samar da wutar latantarki ga jama’ar kasar. Rabin wadannan kudade tallafi ne yayinda dayan bangare ke matsayin rance daga bankin duniya sai sama da wasu million 7 na dolar Amurka da wani asusun tallafi ya bai wa Nijer kyauta.

A yayin da take saka hannu akan wannan yarjejeniya Mme Clara De Souza ta bankin duniya ta bayyana cewa, “Wannan yunkuri wata gudunmuwa ce da za ta taimaka a bunkasa hanyoyin samar da wutar lantarki a Nijer inda ake hasashen ba kashi 60 daga cikin 100 na al’umarta wutar lantarki kafin shekarar 2030 tare da kudirin ganin kashi 40 daga cikin 100 sun sami wutar kafin shekarar 2025“

A cewar Ministan fasali kasa Rabiou Abdou ta hanyar wannan shiri mai lakanin pojet haske, za a karfafa wasu daga cikin layukan wutar lantarkin manya da matsakaitan da ake da su a wannan kasa yayinda a daya bangare za a zuba wadanan kudade don samar da wutar lantarki da hasken rana a biranen da karkara.

Wannan yarjejeniya na zuwa a wani lokacin da Kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi ke taro domin nazarin hanyoyin bunkasa fannin makamashi a Nijer musamman batun samar da wutar lantarki ta hasken rana saboda haka ne Muryar Amurka ta tuntubi Hamidou Sidi Fody na kungiyar CODDAE don jin yadda yake kallon wannan hadin guiwa na bankin duniya da gwamnatin Nijer in da ya su yi na’am da wannan shiri, sabodo lantarki na muhimanci don yara sa samu koyo da ma likotici su samu yin aiki ba tare da matsala ba.

An dai bayyana cewa kauyuka fiye da 500 da birane 79 na kasar nan ne zasu mori aiyukan wannan shiri na Projet Haske.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti :

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
XS
SM
MD
LG