Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya ta kafa dokar ta baci bayan hare hare; an kuma hallaka mutane 50 a jihar Ebonyi


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a ziyarar da ya kai wurin da bam ya tashi

An hallaka akalla mutane 50 a kudu maso gabashin Nijeriya a Jiy

An hallaka akalla mutane 50 a kudu maso gabashin Nijeriya a Jiya Asabar, a wani fadan da aka gwabza tsakanin kabilu biyu da ba sa ga maciji da juna.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Ebonyi ya ce an tura sojoji da ‘yan sanda su kwantar da hankula tsakanin kabilar Ezza da Ezilo da dukkanninsu ke gundumar Ishielu. Ya ce ba a iya tabbatar da adadin mace-macen ba a lokacin.

Dama an cika samin tashe-tashen hankula kan gonaki a wannan kasar da ta fi yawan jama’a a Afirica saboda akasarin ‘yan wannan kasa miliyan 160 manoma ne da ke zaune a kauyuka inda babu cikakkun hukumomin da za su sasanta jama’a.

A halin da ake ciki kuma a jiya Asabar Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci a sassan kasar da rikice-rikice su ka fi addaba.

A wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin a kasar a jiya Asabar, Mr Jonathan ya ce an dau wannan matakin ne a sassan jihar Yobe da Borno a arewa maso gabashin Nijeriya, da kuma jihohin Filato da Naija da ke yankin tsakiyar Nijeriya.

Shugaban na Nijeriya ya ce an kuma rufe kan iyakokin wadannan wuraren da makwabtan kasashe.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG