Accessibility links

Sassan Nijeriya sun shiga sabuwar shekara karkashin dokar ta baci

  • Ibrahim Garba

Wani katon ramin da harin kunar bakin wake ya tona

Tankokin yaki da sojoji na kan sintiri a arewacin Nijeriya bayan da shugaban

Tankokin yaki da sojoji na kan sintiri a arewacin Nijeriya bayan da shugaban kasar ya yi shelar kafa dokar ta baci a wuraren da hare-haren mayakan Islama su ka shafa a baya-bayan nan.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kakaba dokar ranar Asabar a wurare 15 da ke jihohin arewa maso gabashin Yobe da Borno, da kuma jihohin Filato da Naija a yankin tsakiyar Nijeriya.

Kafa dokar ta bacin ya bai ma jami’an tsaro iko kan irin wadannan wurare. Ya kuma hada da rufe kan iyakokin wuraren da kasashen Nijar da Chadi da Kamaru.

Mr. Jonathan, da ya ke jawabi, ya sha alwashin murkushe Boko Haram, wato kungiyar Islamar da ake zargi da kai hare-haren ranar Kirsametin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 40, akasari Kirista.

Ma’anar sunan kungiyar dai shi ne “Ilimin Boko na Yammacin Duniya Haramun ne.” Ta yi ikirarin kai jerin hare-haren bam da harbe-harbe a arewacin Nijeriya da kuma babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

Shugaban kasar ya ce ya umurci Ministan tsaro ya dau matakan da su ka dace a wuraren da abin ya shafa a kasar.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG