Accessibility links

Nijeriya ta sake damke babban wanda ake zargi a harin bam na ranar Kirsimeti

  • Ibrahim Garba

Kabiru Sakkwato

Hukumomin Nijeriya sun sake damke babban wanda ake zargi a

Hukumomin Nijeriya sun sake damke babban wanda ake zargi a harin bam din da aka kai ranar Kirsimeti da ya hallaka akalla mutane 37 a bayan babban birnin tarayyar Nijeriya, Abuja.

Jami’an gwamnati su ka ce Hukumar Binciken Sirri ta Gwamnati ta sake kama Kabiru Sakkwato a yau Jumma’a a jihar Taraba da ke gabashin kasar da kuma ke kusa da kan iyakar Kamaru. Hukumomi sun ce an tafi da shi Abuja ta jirgin sama.

An yi imanin cewa Kabiru Sakkwato dan tsattsaurar kungiyar Islamar nan ce ta Boko Haram, wadda ta dau alhakin kai harin ran 25 ga watan Disamba kan Majami’ar Katolika ta St. Theresa.

Kabiru Sakkwato ya tsere daga hannun ‘yan sanda a Abuja ran 17 ga watan Janairu, bayan kamunsa na farko. A lokacin ‘yan sanda sun ce wasu gungun mambobin kungiyar ne su ka kwace shi a yayin da ake kai shi wani ofishin ‘yan sandan.

Daga bisani dai Shugaba Goodluck Jonathan ya tilasta wa Shugaban ‘yan sandan da wasu manyan jami’an ‘yan sanda yin ritaya da wuri.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG