Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Shugaban Al'ummar Igbo A Arewa Yace Najeriya Kasa Daya Ce


Kawo, Kaduna, Nigeria

Mazi Dominic Uzu, wanda ya shafe shekaru 39 yana zaune a Arewa, yace wasu baragurbin 'yan siyasa ne ke haddasa irin fitinun da ake fuskanta

Wani babban shugaban 'yan kabilar Igbo a yankin arewacin Najeriya ya shawarci 'yan kasar da su ci gaba da zaman lumana da juna, yana mai yin watsi da masu neman wargaza kasar ko neman tayar da fitina a tsakanin kabilunta.

Mazi Dominic Uzu, ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa ne ke zuga matasa su na tayar da fitina a yunkurinsu na cimma wasu gurorin siyasar da suke ganin ba zasu iya cimmawa ba idan hankula su na kwance.

Shugaban na 'yan kabilar Igbo a Kaduna, wanda ya shafe shekaru fiye da 39 yana zaune a arewa, yace Arewa da dukkan al'ummarta 'yan'uwa ne a gare shi, kuma gida ne yankin a wurinsa, har ma yayi misali da wasu Hausawa abokansa wadanda mahaifinsa ya ba su fili suka yi gida, suka kuma yi iyali a yankin Igbo, kuma har yanzu su na zaune a can.

Saurari hirar Mazi Dominic Uzu a sama a gefen dama.

Aika Sharhinka

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG