Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Yi Kira Ga Matasa Su Fito Zabe


Barack Obama

Obama ya bukaci daukacin matasa su fita suyi zabe a watan Nuwamba inda ya shaida masu cewa daga cikin matsa 5 da suka isa zabe ne kawai yayi zabe a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2016.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, wanda ba a cika jin duriyar tun da ya bar mulki ya shiga rudanin zabe da akayi a jiya jumma’a inda yace “ya kamata mutane suyi zabe, domin ‘yancin su ya ta’allaka a kan yin hakan”.

Yace kaucewa yin hakan zai iya zama babban hatsari a garesu baki daya.

Tsohon shugaban na Amurka dai yayi magana ne a lokacin da yake wa dalibai a jami’ar jihar Illions dake Urbana, jawabi inda ya karbi lambar yabo ta kwazo da akida a aikin gwamnati.

Obama ya kara da cewa halin da siyasar Amurka ke ciki yanzu, ba wai ya fara a zamanin Donalad Trump bane, amma yana daya daga cikin alamomi da yace sun matsalolin da ‘yan siyasa suka fara haifarwa a shekarun baya ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG