Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Burtaniyya a Najeriya Ya Kaddamar Da Wata Gasa Don Karrama Ranar Mata Ta Duniya


Ofishin jakadancin Burtaniyya a Najeriya zai ba mata matasa ‘yan 'yan shekara tsakanin 18 zuwa 23 damar aiki da jakadiyar Burtaniyya a Najeriya tsawon yini guda. yayin da aka kaddamar da gasar British High Commissioner For A Day a Abuja.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Burtaniyya a Najeriya ya fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa gasar wani bangare ne na gudanar da wasu shirye shirye don bikin ranar mata ta duniya ranar 8 ga watan Maris na wannan shekarar, da kuma bikin cika shekara 70 akan karagar mulki da za a yi wa Sarauniyar Ingila.

Sanarwar ta kara da cewa wanda ya lashe gasar zai samu damar yin aiki da babban jami’I ko jami’ar diflomasiyyar Burtaniyya a Najeriya tsawon yini guda kuma zai fahimci yadda ake harkokin shugabanci.

Taken ranar mata ta duniya a bana dai shi ne "samun daidaito a yau don makoma mai dorewa."

A bisa haka ne ofishin jakadancin na Burtaniya ya ce an shirya gasar ne da nufin karfafa gwiwar mata matasa su zama jagorori da masu rajin kawo sauyi.

Da take bayani game da gasar, babbar jami’ar diflomasiyyar Burtaniyya a Najeriya Catriona Laing, ta bayyana farin cikin kaddamar da gasar zama babban jami’in a Ofishin na rana guda. karfafa daidaito tsakanin maza da mata da kuma taimaka wa mata na ɗaya daga cikin abubuwan da muka fi ba fifiki a ofishin.

Ta kara da cewa ofishin ya kudurin aniyar taimaka wa mata matasa a fadin Najeriya don su bada gudummowar su akan batutuwan da ke faruwa a duniya da za su taimaka wajen gina makoma mai dorewa ga kowa.

Ms. Laing ta kuma yi kira ga 'yan mata tsakanin shekara 18 zuwa 23 da su shiga wannan gasa ta kuma ce suna fatan jin kyawawan ra'ayoyin su da za su yi tasiri a duniya.

Ana sa ran ‘yan takarar gasar za su yi yi bidiyo na minti daya su bayyana “irin kyakkyawan sauye-sauyen da za su so su gani ta fannin yaki da sauyin yanayi da kuma yadda za su bada gudummowar su.

Bayan haka ana so su yada bidiyon a shafukan sada zumunta kuma ranar 27 ga watan Fabarairu za a rufe shiga gasar.

XS
SM
MD
LG