Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Omicron: Najeriya Ta Bayyana Rashin Jin Dadin Sanya Ta A Jerin Kasashen Haramta Zirga-Zirga Da Burtaniya Ta Yi


Osagie Ehanire
Osagie Ehanire

Ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin Burtaniya ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ta yiwa lakabi da red list biyo bayan gano nau'in Omicron na cutar COVID-19.

Ministan ya ce gwamnatin kasar ba ta ji dadin yadda lamarin ya kasance ba a lokacin da aka sanya kasashe shida a yankin kudu da hamadar Sahara a cikin jerin kasashen da ake kaffa-kaffa da su, duk da cewa hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ba da shawarar a guji yin hakan don gudun maida lamarin kyama ta fuskar kiwon lafiya.

Ministan ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels, kwana guda bayan da kasar Birtaniya ta sanar da daukar matakin, ya na mai cewa akwai matakan kariya na daban da za’a iya dauka ba tare da kakabawa kasashe takunkumi mai tsauri kamar haka ba.

Minista Osagie ya yi misali da cewa ba'a sami asarar rayuka ba kuma har ila yau ba'a sami rahoton rashin lafiya mai tsanani a Najeriyar ba.

"A hakikanin gaskiya saurin daukan matakin sanya kasashe cikin jerin red list da kasar Burtaniya ta yi ba abu ne da zai taimaka a yaki da cutar korona birus ba" in ji ministan.

A cewar ministan, matakin bai dace ba saboda ya lura cewa zai yi tasiri sosai kan harkokin kasuwanci, da kuma kawo cikas ga shirin da iyalai kan yi a lokacin bukukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara don haduwa da yan uwa a yayin da mutane ke mutunta ka’idojin da gwamnatoci suka gindaya.

Osagie ya kuma yi bayanin cewa a lokacin da Najeriya ta gano kwayar cutar COVID-19 a kan matafiya daga kasar Burtaniya, ba'a tabbatar da cewa nau’in Omicron ba ne.

A yayin da yake nanata cewa sanya kasashe cikin jerin red list ba zai taimaka ba wajen yaki da cutar a duniya, Ehanire ya ce Najeriya na sa ran bullar cutar a karo na hudu a halin yanzu.

Haka kuma, ministan ya ce idan kowace kasa za ta sanya wasu kasashe cikin jerin takunkumi, nan ba da jimawa ba Butaniya za ta sanya kasashe da yawa a cikin jerin, kuma ya kamata a samo wata hanya ta daban don yaki da nau’in Omicron ba ta wannan matakin da Burtaniyya ta dauka ba.

Matakin na Burtaniya ya zo ne kwanaki kadan bayan da Najeriya ta gano sabon nau’in cutar korona wato Omicron, kuma hakan ya biyo bayan makamancin matakin da hukumomin Canada suka dauka a baya-bayan nan.

Wannan matakin da Burtaniya ta dauka ya jefa wata daliba yar Najeriya, Zainab Adam da ta sayi tikitin zuwa kasar Canada fara karatu cikin shakku sakamakon yadda ta siyo wani tikitin na daban kan tsabar kudi sama da naira miliyan daya zuwa kasar Burtaniya ta shafe kwanaki 10 daga bisani ta ketara zuwa Canada kafin saka takunkumin na Burtaniya a ranar asabar.

Wani matafiyi, Abubakar Sani, da ya riga ya sayi tikitin zuwa ganin iyalinsa a ranar 15 ga watan disamba a kasar Burtaniya bayan kwashe tsawon watanni bai sa su a ido ba ya bayyana rashin jin dadinsa a game da matakin kasar ta Burtaniyya ya na mai cewa dole ya dakatar da tafiyar ta sa saboda gudun matakai masu tsauri da ka iya biyo bayan wannan.

Baya ga Najeriya, kasashen Masar da Malawi su ne sauran kasashen da aka sanya cikin jerin kasashen da aka saka wa takunkumin hana tafiye-tafiye na Kanada na kwanan nan.

Ana dai rade-raden cewa akwai yiyuwar kasar Burtaniyya ta sake nazari a kan matakin nata zuwa ranar 20 ga watan Disambar da mu ke ciki.

XS
SM
MD
LG