Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Orlando: Abinda Muka Sani Ya Zuwa Yanzu


Omar Mateen mai shekaru 29 ya bude wuta ya kashe mutane 49 jiya lahadi da asuba a Orlando, Florida, yayin da wasu mutanen su 53 suka samu raunuka.

Abubuwan da suka bayyana game da hari mafi muni da aka taba kaiwa kan fararen hula a tarihin Amurka, sune:

Wani matashin da 'yan sanda suka ce sunansa Omar Mateen, mai shekaru 29 da haihuwa, ya kashe mutane 49 da asubahin lahadi a wani gidan rawa dake birnin Orlando a Jihar Florida. Wasu mutanen su 53 sun ji rauni, wasunsu munanan raunuka, kuma su na asibitocin dake yankin.

Akwai mutane fiye da 300 cikin wannan kulob mai suna Pulse a lokacin, suna bukin daren jinsin Latino, ko Latin Night a turance. Jim kadan a bayan da aka fara harbe-harbe da misalin karfe 2 na dare, misalin karfe 7 na safiyar lahadi agogon Najeriya, an rubuta sako a shafin kulob din na Pulse a Facebook inda aka ce "Kowa ya fita ya gudu daga cikin Pulse."

Hukumomi sun ce Mateen yayi amfani da karamar bindiga, da kuma wata babbar bindiga samfurin AR-15 a lokacin wannan farmaki na tsawon awa 3. Yayi garkuwa da mutane 30 wadanda 'yan sanda suka ceto. Mateen ya mutu da misalin karfe 5 na asubahi, watau karfe 10 na safiya agogon Najeriya, a musanyar wuta da zaratan 'yan sanda na rundunar SWAT.

Magajin garin birnin Orlando, Buddy Dyer, ya bayyana jiya lahadi a zaman "rana mafi alhini" a tarihin birnin.

Omar Mateen ya kira lambar neman taimakon gaggawa, watau 9-1-1, inda yayi ikirarin yin mubayi'a ga kungiyar Daesh ko ISIS. Daga baya kungiyar ta fada ta wata kafar labaranta cewa wani mayakinta ne ya kai harin. Sai dai ba a san ko wace irin alaka ke tsakaninsa da kungiyar ba, idan ma har akwai din.

A shekarun 2013 da 2014, hukumar Binciken manyan laifuffuka ta tarayya, FBI, ta yi ma Mateen tambayoyi, amma masu bincike ba su gano wata alamar cewa yana karya doka ba. Wakilin hukumar FBI, Ronald Hopper, yace an yi zargi a lokacin cewa Mateen yana rungumar akidar tsageranci ta addini.

'Yan sandan birnin Orlando sun saki sunayen kimanin rabin mutanen da aka kashe, wadanda aka samu damar sanar da iyalansu ke nan cewa ga abinda ya same su. Wadanda suka mutun shekarunsu ya kama daga 20 zuwa 50.

XS
SM
MD
LG