Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osinbajo Ya Gana Da Dakatun Tsaron Najeriya


Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron kasar.

Mukaddashin shugaban na Najeriya, yayi wata ganawa ta musamman tsakaninsa da dakarun tsaron kasar, wanda suka hada da masu fada aji kan tsaro, masu kaki da masu farar hula domin samun cikakken bayani game da halin da kasar ke ciki dangane da matakan tsaron da ake dauka na samar da zaman lafiya.

Ministan tsaro na Najeriya, Janar Mansur Dan Ali, yace taron an tattauna kan nasarar da ake samu a yaki da ake kungiyar Boko Haram. An kuma tattauna game da rikicin dake faruwa a Yammacin Kaduna, inda aka yanke hukuncin ‘kara sojoji a yankin.

Batun Niger Delta na ‘daya daga cikin abubuwan da aka tattaunawa a wannan ganawa da mataimakin shugaban ‘kasa, inda ana samun ci gaba wajen samar da sulhu a yankin mai albarkatun Man fetur.

Anyi maganar samar da kotuna masu yawa domin a samu gurfanar da mutanen da aka kama ba tare da bata lokaci ba, kasancewar yawan mutanen da ke hannu jama’an tsaro ba tare da gurfanar da su ba.

Domin karin saurari rahotan Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG