Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pantami Ya Shiryawa Fani-Kayode, Matawalle Liyafa A Gidansa


Matawalle, hagu, Pantami, tsakiya da Fani-Kayode a dama (Facebook/Fani-Kayode/ Onevoiceafrica)

A ranar Juma'a Fani-Kayode, wanda ya yi fice wajen sukar lamirin gwamnatin Buhari, ya koma jam'iyyar APC mai mulki yayin da shi kuma Matawalle tun a watan Yuli ya koma jam'iyyar.

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin fasahar zamani Dr. Isa Ali Pantami, ya gayyaci Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, Femi Fani-Kayode cin abincin dare a gidansa.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta don nuna godiyarsu bisa wannan gayyata, Fani-Kayode ya jinjina gayyatar da ministan ya yi musu.

A ranar Juma'a Fani-Kayode ya koma jam'iyyar APC mai mulki yayin da shi kuma Matawalle tun a watan Yuli ya koma jam'iyyar.

“Wannan babbar girmamawa ce a madadina da abokina gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da Ministan Sadarwa da bunkasa tattalin arzikin fasahar zamani Prof. Isa Ali Pantami ya gayyace mu zuwa cin abincin dare a kayataccen gidansa a daren jiya (Juma’a).

Matawalle da Fani-Kayode a gidan Pantami (Facebook/Fani-Kayode/onevoice africa)
Matawalle da Fani-Kayode a gidan Pantami (Facebook/Fani-Kayode/onevoice africa)

“Mun jima a gidan har zuwa kusan wayewar gari, inda muka tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa da yadda za a samu mafita.

“Na gode da wannan gayyata dan uwa. Tare, za mu ci gaba da dabbaka zaman lafiya, hadin kai, kauna a wannan kasa ta mu, mu kuma yaki ayyukan ta’addanci tare da farfado da kimar Najeriya. Akwai alkhairai a gaba da za a gani.” Fani-Kayode ya ce.

Gayyatar da Pantami ya yi wa Fani-Kayode da Matawalle, na zuwa ne jim kadan bayan da (Fani-Kayode) ya koma jam’iyyar APC inda har aka gabatar da shi ga shugaba Muhammadu Buhari a Aso Rock, lamarin da ya janyo ka-ce-na-ce a sassan Najeriya.

Shi dai Fani-Kayode, ya kasance mai amfani da zafafan kalamai wajen sukar lamirin gwamnatin Buhari da mukarrabanta kamar yadda rahotanni kan nuna.

A shekarun baya ya taba wallafa cewa, da ya koma jam’iyyar ta APC mai mulki gwamma ya mutu.

Fani-Kayode ya caccaki Pantami a Watan Afrilu, a lokacin da wasu kafafen yada labarai suka ruwaito cewa Amurka ta saka shi (Pantami) a jerin wadanda ke goyon bayan Al Qaeda saboda wası kalamai da ya yi a baya, zargin da Pantamin ya musanta ya kuma fito ya kare kansa.

Fani-Kayode (na farko daga dama, sanye da jan kaya) a fadar shugaban kasa
Fani-Kayode (na farko daga dama, sanye da jan kaya) a fadar shugaban kasa

Hakan ya sa bullar wasu hotuna dauke da Fani-Kayode da Pantamin suna raha a lokacin daurin auren dan shugaban kasa Yusuf Buhari a watan Agusta, ya ja hankalin 'yan Najeriya, inda tun daga lokacin aka fara hasashen tsohon ministan sufurin na shirin komawa jam'iyyar ta APC.

Komawar jam’iyyar da ya yi a ranar Jum’a, ta sa an yi ta caccakar shi kan yadda ya yi amai ya lashe, inda kafafen yada labarai da jama’a da dama suka yi ta zakulo wallafe-wallafe da kalamai da ya yi baya, inda yake sukar gwamnatin Buhari.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels bayan da ya koma APC, Fani-Kayode ya ce matakin da ya dauka bai sabawa kowa ba, saboda haka ba wanda yake bin shi bashin neman afuwa.

“Abubuwa da dama sun canja cikin shekara 6, yana da muhimmancin mutum ya dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace, musamman idan Allah ne yake karkata hankalin kan hakan. Ni na san cewa na yi abin da ya dace ne.” Fani-Kayode ya fadawa Channels.


XS
SM
MD
LG