Accessibility links

PDP Ta Ci Zaben Dan Majalisar Wakilai A Jihar Adamawa

  • Ibrahim Garba

Alamar Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Adamawa da Nijeriya

Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Adamawa da Nijeriya ta ci zaben Majalisar Wakilai na cike gurbi da aka gudanar jiya Asabar a jihar Adamawa.

Jam'iyyar PDP mai mulki ta lashe zaben cike gurbi na Majalisar Wakilai mai wakiltar Nasarawo da Binyeri a jihar Adamawa da aka gudanar jiya Asabar. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC) ta ba da sanarwar cewa dan takarar jam'iyyar PDP Alhaji Umaru Abdulkarim ya ci zaben da kuri'u 12,040.

Wakilin Muryar Amurka a jihar ta Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ya aiko da rahoton cewa Kwamishinan hukumar ta INEC a jihar ta Adamawa Barrister Kasim Gana Gaidam ya yaba da yadda mutane su ka ba da hadin kai lokacin zaben har aka yi shi cikin kwanciyar hankali.

Ibrahim Abdul'aziz ya ruwaito dan takarar jam'iyyar ACN Mr. Yohana Mathias na cewa ya dauki zaben tamkar gasar kwallo ce. Ko ka yi nasara ne ko kuma wani daban ya yi.

XS
SM
MD
LG