Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Kasa Gudanar Da Zaben Fidda Ƴan Takarar Neman Kujerar Gwamna A Jihar Neja


Taron majalisar zartarwar jami'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: PDP).
Taron majalisar zartarwar jami'iyyar PDP a Najeriya (Hoto: PDP).

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kasa gudanar da zabenta na fidda gwani na masu takarar kujerar gwamna da ta shirya gudanarwa a ranar laraban nan a jihar Neja. Al’amarin da ya raba kan 'yaƴan jam’iyyar ta PDP gida 2.

Wasu daga cikin 'yantakara ne dai suka bukaci masu zaben yantakatar na PDP da su yi amfani da katin zabe ko national ID card ko kuma E-pasport domin kada kuri’ar su.

Tsohon Ministan wajen Nigeria, Alh. Abubakar Tanko yace basu taba gani irin wannan tsari ba.

Lawyan PDP a jihohin Arewa ta tsakiyar Nigeria Barista Isyaku Barau yace tsarin bai sabawa kundun tsarin Mulkin PDP ba.

Shugaban PDP na jihar Neja, Barista Tanko Beja yace za a gudanar da zaben a ranar Alhamis din nan.

Mataimakin Gwamnan Bayalsa Laurance Obarawharienwo da PDP ta turo jihar Nejan, ya tabbatarwa manema labarai cewa, zasu warware duk wasu matsalolin da su ka yi tarnaki a zaben.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG