Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Peter Obi Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A Jihar Legas 


Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a Najeriya, Mr. Peter Obi

Dan takarar shugabancin Najeriya, Peter Obi, wanda yakin neman zabensa ya ja hankulan matasa da masu kada kuri'a a biranen kasar da suka koka da gurbatacciyar siyasa, ya lashe mafi yawan kuri'u a cibiyar kasuwanci ta jihar Legas, inda birni mafi girma a Afirka yake. 

A ranar Lahadi ne hukumar zaben Najeriya ta fara bayyana sakamakon jahohi a zabukan kasar, ko da yake ba a sa ran za ta bayyana wanda ya lashe zaben shugabancin kasar ba.

Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 582,454, wanda ke gaban tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, da kuri’u 572,606, kamar yadda bayanan hukumar zaben suka nuna a ranar Litinin. A baya Legas ita ce babbar tungar Tinubu.

Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’u 75,750.

Kamfen din Obi ya yi kira ga masu kada kuri’a da su yi watsi da jam’iyyun biyu da suka jagoranci kasar, wadanda cin hanci da rashawa ya yi kamari a karkashinsu, kuma rashin tsaro ya bazu a fadin kasar.

Ya fi karbuwa a wurin matasa, amma musamman na cikin birane, masu jefa kuri'a da ke da ilimi wadanda ke da damar yin amfani da wayoyin hannu da kafofin watsa labarai. Amma har yanzu yana fuskantar matsaloli a yankunan karkara masu saukakakkiyar rayuwa.

XS
SM
MD
LG