Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Na Karbar Bakuncin Shugabannin Kasashen Afrika


A wannan mako ne shugaban Rasha, Vladimir Putin, zai karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da dama a wani wurin shakatawa da ke garin Sochi inda za su gudanar da wani taron kwanaki biyu.

Wannan taro, shi ne na farko da shugabanin kasashen nahiyar ta Afirka za su halarta a Rasha, tun bayan rugujewar Tarayyar Soviet a shekarar 1991.

Kamar yadda jami’an Fadar gwamntin Kremlin suka bayyana, taron zai mayar da hankali ne wajen yin karin haske kan dalilin da ya sa Rasha ta sake mayar da hankalinta kan nahiyar ta Afirka, tare da nunawa shugabanninta cewa Rasha ta farfado daga kallon da ake mata na kasar da ta durkushe.

A makon da ya gabata, Kakakin Shugaba Putin, Dmitry Peskov, ya fadawa manema labarai cewa, Rasha na da abubuwan da za su karfafa dangantakar da takwarorinta na nahiyar Afirka.

Wata sanarwa da dauke da sa hannun mai bai wa Shugaba Najeriya, Muhammadu Buhari, shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu, ta nuna cewa tuni shugaban Najeriya ya isa garin na Sochi.

A cewar sanarwara, taron zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG