Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Kaddamar Da Hare-hare A Kan Ukraine


Kyiv, Ukraine
Kyiv, Ukraine

Shugaba Putin ya kuma yi gargadin cewa kada wata kasa ta tsoma bakinta a cikin wannan lamari.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kaddamar da hare-hare a gabashin Ukraine da safiyar Alhamis, yana mai cewa ya dauki matakin ne a matsayin martani ga barazanar da Ukraine ta yi.

Hare-haren na Rasha na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Rashar ta ayyana wasu yankunan kasar ta Ukraine biyu a matsayin masu cin gashin kansu, inda ta tura dakarunta da sunan kare lafiyar al’umomin yankunan.

Yayin da yake sanar da sabon mataki da suka dauka da safiyar yau Alhamis, Putin ya ya gargadin kasashen duniya da kada su tsoma baki a lamarin.

Cikin wata sanarwa da ya yi ta kafar talabijin, Putin ya ce duk wadanda suke adawa da matakin da Rasha ta dauka a yankin Donbas, za su fuskanci “mummunan sakamakon da ba su taba gani ba.”

Rahotannin sun ce an ji karar fashe-fashe a Kyiv, babban birnin kasar ta Ukraine.

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada cikin wata sanarwa cewa, al’umar Ukraine na shan wahala “daga hare-haren da dakarun Rasha ke kai wa, ba tare da sun tsokani kowa ba.”

Biden ya kara da cewa, zai tattauna da shugabannin kungiyar G-7 da safiyar Alhamis, kafin su sanar da “karin matakan da Amurka da kawayenta da abokan huldarta za su dauka akan Rasha, bisa wannan muzgunawa da take yi wa Ukraine da barazana ga zaman lafiya a duniya.”

XS
SM
MD
LG