Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Kada Ku Yi Tsammanin Za Mu Maida Hankali Kan Messi Ne Kadai A Wasan Daf Da Na Karshe - Croatia


Dan wasan Argentina Lionel Messi
Dan wasan Argentina Lionel Messi

Croatia ta ce, ba za ta yi yunkurin mai da hankali kan dan wasan Argentina Lionel Messi shi kadai ba, amma a maimakon haka za ta mayar da hankali wajen hana daukacin 'yan wasan baki dayansu a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin duniya ranar Talata.

Kasar Croatia na neman zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya karo na biyu a jere bayan da ta sha kashi a wasan cin kofin a 2018 da Faransa.

Sun bai wa Brazil mamaki a gasar wasan daf da na kusa da karshe bayan da ta zura kwallo a raga a cikin karin lokaci amma sai suka zura kwallo a ragar Brazil da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Yan wasan Croatia
Yan wasan Croatia

"Har yanzu ba mu da wani takamamman shiri na dakatar da Messi kuma yawanci ba ma mayar da hankali wajen dakatar da dan wasa daya shi kadai, sai dai daukacin kungiyar baki dayansu," in ji dan wasan gaban Bruno Petkovic a wani taron manema labarai jiya Lahadi.

Yan wasan Argentina
Yan wasan Argentina

"Za mu yi kokarin dakatar da su a kungiyance ba tare da nuna alamar mutum daya ba. ‘Yan wasan Argentina ba Messi kadai ba ne, suna da manyan 'yan wasa da dama, dole ne mu dakatar da dukan 'yan wasan Argentina."

Lionel Messi
Lionel Messi

Kawo yanzu Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai shi ne kan gaba a ‘yan wasan na Argentina, wadanda su ma suka bukaci bugun fanariti bayan da suka kasa zura kwallaye biyu a ragar Holland a wasan daf da na kusa da na karshe.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG