Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Qatar 2022: ‘Yan wasan Da Ba Za Su Halarci Gasar Cin Kofin Duniya Ba


Dan wasan Norway/ Manchester City, Erling Haaland (AP)
Dan wasan Norway/ Manchester City, Erling Haaland (AP)

Za a fara gasar da wasan Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da mai cin 'yan kallo dubu 60.

A ranar 20 ga watan Nuwamba za a bude gasar cin kofin duniya ta FIFA a kasar Qatar wacce kuma za a kammala a ranar 18 ga watan Disambar bana.

Za a fara gasar da wasan Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt da mai cin 'yan kallo dubu 60.

Sai dai yayin da ake shirin fara karawa a gasar, akwai fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya da ba za su halarci gasar ba saboda dalilai daban-daban, ga kadan daga cikinsu:

Erling Haaland (Norway) - Dan shekara 22, Haaland ya fara kakar wasan bana a sabuwar kungiyarsa ta Manchester City da kafar dama, inda ya zura kwallaye 17 a wasanni 11 a gasar Premier League. Sai dai kasarsa ta asali, wato Norway, ta gaza samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya bayan da ta kasa doke Netherlands a wasannin fidda gwani a rukunin G.

Paul Pogba (Faransa) - Dan wasan Faransa, Paul Pogba ba zai samu zuwa gasar ta cin kofin duniya ba, bayan da aka sanar da cewa yana fama da ciwo a kwaurinsa. Dan shekara 29, Pogba ya taka muhimmiyar ruwa a nasarar lashe kofin gasar, wanda Faransa ta lashe shekaru hudu da suka gabata.

Paul Pogba
Paul Pogba

Mohamed Salah (Egypt) - Shi ma Mohamed Salah na kasar Masar,a ba zai samu zuwa gasar ba saboda Senegal ta doke ta a bugun fenariti a wasannin fidda gwani. Salah, wanda jigo ne a kungiyar Liverpool, ya lashe kyautar ‘Golden Boot’ ta dan wasan da ya fi zura kwallo a gasar Premier a kakar wasa ta bara.

Mohamed Salah
Mohamed Salah

N’Golo Kante (Faransa) - Kante ya kwashe tsawon lokaci bai bugawa kasarsa wasa ba tun watan Agusta. A watan da ya gabata ne kungiyarsa ta Chelsea ta sanar da cewa dan wasan tsakiyar ba zai buga gasar ta cin kofin duniya ba saboda yana jinyar wani aiki da aka masa a bayan cinyarsa.

N'Golo Kanté
N'Golo Kanté

David Alaba (Austria) - Ita dai kasar Austria ba ta samu gurbin shiga gasar ta cin kofin duniya ba, bayan da Wales ta doke ta. Gareth Bale ya ci kwallaye biyu a wasan da aka tashi 2-1 wanda ya hana Alaba zuwa gasar.

David Alaba
David Alaba

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG