Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Mutane Sun Bambanta Kan Umurnin ECOWAS Ga Sojojin Nijar


Taron Shugabannin Kungiyar ECOWAS kan juyin mulki da sojoji su ka yi a Nijar
Taron Shugabannin Kungiyar ECOWAS kan juyin mulki da sojoji su ka yi a Nijar

Jama'a na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta game da matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da umarnin su maida mulki hannun farar hula.

Matakin na ECOWAS ya zama abun nazari da tattaunawa ga masu sharhi inda wasu ke cewa kungiyar ta yi tsauri yayin da wasu ke cewa daidai ne.

Shugaban majalisar amintattu ta kungoyoyin arewa Nastura Ashir Sharif na cewa matakin zai takura rayuwar talakawa ne da yiwuwar fadawa irin yanayin fitinar kasar Sudan.

Niger Coup
Niger Coup

Nastura Sharif ya ba da shawarar kafa kwamitin dattawa na tsoffin shugabannin kasashen ECOWAS don su je Niamey su samar da maslaha.

Shi kuma Shu'aibu Gabchari wanda tsohon shugaban karamar hukumar Darazo ne a jihar Bauchi ya ce ya goyi bayan ECOWAS don ta hakan ne za'a sami sakamako a takadirin lokaci.

Gabchari ya bugi kirjin cewa duk jama'ar Afirka na marawa shugaba Bazoum baya.

Shugaba Mohamed Bazoum
Shugaba Mohamed Bazoum

A na sa sharhin dan jamhuriyar Nijar mazaunin Abuja Abubakar Khalidou ya ce Bazoum ya yi karambani a kalaman da ya furta na neman janyewa daga Faransa.

Khalidou ya ce bai yi mamakin abun da ya faru ba don Nijar mutum biyu ke mulki da babba da karami.

Hakanan Khalidou ya bukaci a bar sojojin su shekara biyu kan karagar mulki kafin sanin mataki na gaba.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG