Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Juye-Juyen Mulki a Nijar


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Ana ci gaba da samun ra'ayoyi mabambanta  game da juyen mulki da wasu sojoji a karkashin jagorancin Janar Abdurahamane Tchiani suka gudanar a cikin wannan makon a Jamhuriyar Nijar.

Jamhuriyyar dai ta Nijar ta yi kaurin suna a kasashen duniya game da yawaitar juye-juyen mulki a kasar da ta fuskanci juye-juyen mulki har guda biyar.

Shugaban kasar na farko da ya fara fuskantar juyin mulkin, shine marigayi Diori Hamani, wanda Laftana Kanar a wannan lokacin marigayi Seyni Kountche ya hambare, a ranar 15 ga wata Afrirulu shekarar 1974, wanda shima kuma ya sha fuskantar yunkurin juyin mulki akalla uku, a shekarar 1975 da 1976 da kuma 1983, kafin ya rasu a ranar 10 ga watan Novemba na shekarar 1987.

Daga bisani ne manyan sojojin kasar Nijar suka maye gurbinshi da marigayi Janar Ali Chaibou, shugaban Hafsan sojojin Nijar a wannan lokacin.

A shekarar 1991, an samu gudanar da babban taron mahawara na ‘yan kasa da ake kira "conference Nationale," wanda ya baiwa Jamhuriyyar Nijar damar kafa mulkin Dimokradiyya, ta hanyar samun jam’iyyun siyasa barkatai.

Hakan ya baiwa Mahamane Ousmane damar kasancewa shugaban kasar Nijar a shekarar 1993.

Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar
Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

Bayan mulkin shekaru uku kachal, marigayi Kanar Ibrahim Bare Mainasara ya hambare shi a ranar 27 ga watan Janairu na shekarar 1996, wanda shima marigayi Daouda Malam ya wanke shugaban rundunar dogarawan fadar shugaban kasa, ya hambare a ranar 9 ga watan Afirulu na shekarar 1999.

Ya kuma amince ya mika mulki ga farar hula bayan ya kammala mulkin na rikon kwarya na tsawonn watani tara. Hakan ya baiwa marigayi Tanja Mamadou damar kasancewa shugaban kasa a ranar 24 ga watan Novemba na shekarar 1999 wanda shima Janar Salou Djibo ya hambare a ranar 18 ga watan Fabrairu na shekarar 2010 bayan yunkurinsa na tazarce.

Tsohon Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou
Tsohon Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou

Issoufou Mahamadou Shugaban jam’iyyar PNDS Tarayya ya hau karagar mulki bayan zaben shekarar 2011, wanda bayan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kamar yadda kundin tsarin mulki jamhuriyyar Nijar ya ayyana, ya shirya zaben da yMohamed Bazoum ya lashe aka rantsar a matsayin Shugaban kasa a shekarar 2021, wanda shima a gab da rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban kasar aka samu wani yunkrin juyin mulki da rundunar dogarawan fadar shugaban kasa suka murkushe.

Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum

Juyin mulkin baya bayan nan shine na ranar Laraba 26 ga watan nan na Yuli shekarar 2023, wanda Janar Abdurahammane Tchini ya jagoranta wanda shine shugaban dogarawan fadar shugaban kasa, kuma tsohon shugaban rundunar fadar shugaban kasa a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou.

A yanzu dai ana iya cewa, Jamhuriyyar Nijar ta yi kaurin suna wajen juyin Mulki a Nahiyar Afrika musamman ma a yankin yammacin Afrika.

A hirar shi da Muryar Amurka, Mahamane Bachar mai fashin bakin al’amuran yau da kullum a jamhuriyar ta Nijar ya yi karin haske game da dalilai da ke kawo yawaitar juye -juyen mulki a Jamhuriyyar ta Nijar.

Rashin gudanar da kyaukyawa mulki na cikin manyan dalilan dake kawo juyin mulki saboda a lokacin da mulkin dimokradiyya ya zo a kasashen Afrika, ana kwantanta wa kamar ana gudanar da mulkin na Dimokradiyya ne, amma a zahiri mai karfi ne ke samun mulki sannan mafi yawa 'yan siyasa na gudanar da mulkin kama-karya ne, to mafi yawan sojoji na amfani da wadannan dalilan wajen kiffar da wata Gwamnatin farar hula

A nashi bangaren, Aisani Tchiroma memba a wata kungiyar farar hula da ake kira ROTBA a Jamhuriyyar ta Nijar ya ce:

Abu na farko dai shugaban da aka hambare na samun cikas wajen gudanar da tsarin da ya zo da shi, sannan juyen mulki na kawo makara wajen aiwatar da wasu matakai na ci gaban kasa musamman ma na kasa da kasa, kuma juyin mulki na bada damar kawo sabbin kanu waje jagoranci wadanda basu lakanci aikin ba.

A yanzu ‘yan kasar ta Nijar na zaman jiran matakin da kungiyar kasahen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO zata dauka a taron na yau Lahadi a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya game da juyin mulkin baya- bayan na kasar.

Saurari rahoton Yusuf Abdullahi a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG