Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayin Shugaban Turkiyya Da Na Girka Ya Sha Bambam Akan Yarjejeniyar Lausanne


A gobe Juma’a ake sa ran shugabban Turkiyya Recep Tayyip Erdogon zai fara ziyara a yankin Thrace dake kasar Girka.

A yau Alhamis Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce akwai bukatar a sabunta wata yarjejeniya da aka cimma a shekarar 1923, wacce ta shata iyakar kasar da sauran makwabtanta.

Erdogan ya yi wadannan kalaman ne yayin wata ganawa da suka yi da shugaban Girka, Prokopis Pavlopoulos ta kafar sadarwar talbijin, gabanin wata ziyarar aikin kwanaki biyu da zai kai Girka.

Shugaban na Girka ya ki amincewa da shawarar ta Erdogan, yana mai cewa yarjejeniyar ta Lausanne, ba ta bukatar a sabunta ta ko kuma a yi mata dauraya.

Shi dai shugaban Turkiyya ya yi kalaman nasa ne lura da cewa akwai Turkawa da ke zaune a wani yankin Girka, inda ya ce ana samun tsirarun Musulmi a Lardin Thrace.

A cewar Erdogan akwai fargabar ko ana basu walwalar gudanar da addininsu ba tare da tsangwama ba.

A gobe Juma’a ake sa ran shugabban na Turkiyya zai fara ziyara a yankin na Thrace.

Zai kuma kasance shi ne shugaban Trukiyya na farko da zai kai ziyara kasar ta Girka a hukumance cikin shekarun da suka gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG