Accessibility links

Ra'ayoyi Kan Nelson Mandela Daga Ghana


Mutane suna waka suna girmama Nelson Mandela yayin da yake jinya

Ga ra'ayoyi kana Nelson Mandela daga Ghana

Mutanen duniya manya da kanana sun cigaba da bayyana ra'ayinsu kan Nelson Mandela tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu wanda ya rasu jiya yana da shekaru casa'in da biyar a duniya.

Abdulrahaman na unguwar fadama ya ce dalilin da ya sa mutanen Afirka Ta Kudu ke matukar kaunarsa domin ya zama uba garesu. Duk wanda ya sauka Afirka Ta Kudu ya ga yadda Nelson Mandela ya samarma 'yan kasar bakaken fata da wadanda basu da tushe 'yanci. Ban da haka Mandela ya shiryawa mutanensa adalci inda babu banbanci tsakanin baki da fari.

Isa Mairago Jibril Abbas ya ce ba komi ba ne illa salon mulki na gari da kuma alheri da ya shuka ma alummar Afirka Ta Kudu shi ya sa suke girmamashi da yi masa daukaka da nuna mashi kauna. Sanadiyar yin mulki na gari da yaki da zalunci duk duniya tana son Nelson Mandela. Gwagwarmayar da yayi da mulkin wariyar launi ta kawo mashi daraja da girmamawa.

Alhaji Gado ya ce suna sonshi domin ya sadakar da kanshi ya kuma sha bakar wahala dominsu. Wannan abun da ya yi masu ya isa su yi mashi komi. Idan al'ummar kasar suka nuna mashi soyayya fiye da haka ba a banza suka yi ba.

Sun yi kwatanci da sauran shugabannin Afirka. Su ka ce mutum ne wanda ya taso bashi da komi amma da zarar ya samu shugabanci sai ya tara ma kansa abun duniya abun da Nelson Mandela bai yi ba.Kafin a ankara sai ya mayar da kansa Allah. Idan aka yi masa wani abu ya fita ya nuna iko ba tare da rangwame ba. Kunsan duk shugabannin Afirka mulkin da turawan mulkin mallaka suka yi shi ne su ma suke yi.

Daga bisani kowa ya yadda cewa Nelson Mandela mutum ne mai yin adalci da aikata gaskiya. Shi ne yayi shugabanci na wa'adi daya ya cewa kasar ta zabi wani ya cigaba. Wannan abun koyi ne ga 'yan siyasar Afirka.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG