Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin Wasu Yan Najeriya Game Da Zaben Amurka


Yan takarar shugabancin Amurka
Yan takarar shugabancin Amurka

Yayin da ake shirye shiryen gudanar da babban zaben shugaban kasa a Amurka, biyo bayan yawan kamfen da ‘yan tarar shugabancin kasar ke yi na ganin sun sami nasara a zaben da za a yi gobe Talata.

Domin jin ra’ayoyin wasu ‘yan Najeriya game da zaben Muryar Amurka ta zagaya jihar Oyo, inda ta fara haduwa da wani mutum mai suna Alhaji Jinaidu Mai Shayi, wanda yayi fatan alkhairi ga zaben ya kuma yi kira ga duk wanda Allah ya baiwa nasara da ya tuna da halin da ake ciki a kasashen Afirka, musamman ma rashin zaman lafiya dake damun Najeriya da makwabtanta.

Adamu Sulaiman sarkin Hausawan Akinyele Ibadan, cewa yayi fatan sa shine Allah ya baiwa Hillary Clinton nasara, domin idan har Donald Trump ya ci to Amurka zata mayar da hankaline a al’amuran da suka shafi yaki, kuma basu taimakawa kasashen Afirka ba.

Shima kuma George Bello, cewa yayi Donald Trump yake so yaga ya samu nasarar zaben na gobe, domin kila ya taimaka a sami daidaiton tattalin arzikin Najeriya, ya kuma ce yana ganin idan Donald Trump ya samu nasara zai taimakawa kasashen Afirka.

Ita kuma Hajiya A Daki Banci Akinyele, cewa tayi dan Allah duk wanda ya ci zaben Amurka a bashi, shi kuma ya taimakawa Buhari kasancewar Najeriya tana cikin wani hali.

Saurari ra’ayoyin ‘yan Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

XS
SM
MD
LG