Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahotanni Na Musamman: Boko Haram


Rahotanni Na Musamman: Boko Haram

http://media.voanews.com/images/boko-haram-480.jpg

Boko Haram Pt. 3
A ci gaba da rahotanni na musamman game da kungiyar Boko Haram, kashi na uku yayi magana kan abubuwa da dama, ciki har da irin matakan tsaron da hukumomi suke dauka domin kawo karshen wannan lamarin.

Kashin Farko (Mohammed Yusuf da Abu Zaid)
A kashin farko na wannan rahoto na musamman, Ibrahim Alfa Ahmed da Halima Djimrao sun duba asali, da kafuwa da kuma akidar wannan kungiyar da mutane suka fi saninta da sunan Boko Haram. Wadanda za a ji muryoyinsu ciki sun hada har da marigayi Malam Mohammed Yusuf, shugaba kuma mutumin da ya kafa wannan kungiya, tare da kakakinta na yanzu, Abu Zaid.

Sheik Mahmud Jaafar Adam Kan Mohammed Yusuf
Sheikh Mahmud Jaafar Adam, shi ne ya koyar da marigayi Malam Mohammed Yusuf, kuma a cikin wannan bayani nasa, za a ji rantsuwar da yayi kan tattaunawar da yayi da tsohon almajirin nasa da yadda ya nemi kawar da shi daga hanyar da ya runguma ta yin fatawar haramcin karatun zamani.

Sheik Jingir
Shugaban kungiyar Jamaatu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa a Najeriya, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yayi magana kan muhimmancin karaytun Boko ga Musulmi da Musulunci.

XS
SM
MD
LG