Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram 11 Sun Bakunci Lahira Inji Jamian Gwamnatin Kasar Najeriya


Goodluck Jonathan shugaban kasar Najeriya wadda matsalar kungiyar Boko Haram ke neman zamewa tuwon tulu
Goodluck Jonathan shugaban kasar Najeriya wadda matsalar kungiyar Boko Haram ke neman zamewa tuwon tulu

Jami'an Sojin Najeriya sun ce an kashe 'Yan Boko Haram 11 Daya a birnin Maiduguri

Jami'an sojojin Najeriya sun ce an kashe 'yan Boko Haram goma sha daya a birnin Maiduguri a arewa maso yammacin Najeriya.

Jami'an sun ce da yammacin ranar asabar aka kashe 'yan Boko Haram din ne a cikin wani fito na fito da sojoji da 'yan sanda.

Sun ce an fara dugumurjin ne lokacin da 'yan Boko Haram su ka jefawa jami'an tsaron da ke sintiri boma-boman da su ka hada da kan su a wurin zaman su.

Kamfanin dillancin labaran "Associated Press" ya ruwaito wani shaidan da ya ce shi dan uwan daya daga cikin wadanda aka kashen ne, ya na cewa, sojoji sun yi awowi su na bin mutane da gudu a kan tituna su na harbin su.

Kungiyar Boko Haram ta na so ne ta kafa tsarin mulkin shari'ar Islama tsantsa kuma a wurare da dama na kasar Najeriya. Jami'an gwamnatin kasar Najeriya na zargin kungiyar da kisan dimbin 'yan sanda da sojoji da malamai da sauran mahukunta a shekarar da ta gabata, musamman ma a Najeriya.

Kwanan nan shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya tura karin daruruwan sojoji birnin Maiduguri.

A halin da ake ciki kuma wata fashewa a wata Majami'ar Suleja, a bayan garin Abuja babban birnin kasar, ta halaka mutane ukku a kalla, kuma ta raunata wasu bakwai a jiya lahadi.

Nan take dai babu wani bayani a kan musababbin fashewar, haka zalika babu wani mahalukin da ya dauki alhakin kai harin.

XS
SM
MD
LG