Accessibility links

Dan Sanda Ya Bindige Yarinya A Maiduguri


'Yan sandan "mobile" na Najeriya su na sintiri a titunan Kaduna lokacin zaben gwamna. Ana zargin daya daga cikin irin wadannan 'yan sandan kwantar da tarzoma da laifin bindige wata yarinya mai shekaru 13 da haihuwa har lahira a Maidugurin Jihar Borno yau

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, wanda ya ganewa idanunsa gawar wannan yarinya kwance a inda aka harbe ta, ya ce mazauna unguwar, wadanda suka nuna alamun harzuka sosai, sun yi zargin cewa haka siddan wannan dan sanda ya bude mata wuta ya kashe ta a idanunsu

Mazauna wata unguwa a tsakiyar birnin Maiduguri, sun fito tituna su na nuna fusatar kisan wata yarinya mai shekaru 13 da haihuwa, wanda ake zargin wani dan sandan kwantar da tarzoma, ko Mobile da aikatawa.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, wanda ya ganewa idanunsa gawar wannan yarinya kwance a inda aka harbe ta, ya ce mazauna unguwar, wadanda suka nuna alamun harzuka sosai, sun yi zargin cewa haka siddan wannan dan sanda ya bude mata wuta ya kashe ta a idanunsu.

Dan majalisar dokokin Jihar Borno mai wakiltar cikin Maiduguri, Abubakar Tijjani, ya shaidawa wakilinmu Haruna Dauda, a cikin fushi a inda wannan lamarin ya faru cewa ko dai gwamnati ta janye wadannan jami'an tsaro dake cin mutuncin mutane, ko kuma zasu yi murabus daga kan mukamansu.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa a Maiduguri, Kanar Victor Ihemele, ya fadawa wakilinmu cewa ba zai ce uffan game da wannan lamarin ba. Amma kuma wakilinmu ya ji shi yana fadawa dan majalisa Abubakar Tijjani mai wakiltar inda wannan lamari ya faru a majalisar dokokin Jihar Borno, cewa sun kama wannan dan sanda da ake zargi su na tsare da shi.

Saurari

Rahoton Haruna Dauda Daga Maiduguri

XS
SM
MD
LG