Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoto Na Musamman Akan Baga: Babi na Daya


Wasu gine-gine da aka kone
Wasu gine-gine da aka kone

Ranar Asabar da asubahin 'yan Boko Haram, 'yan ina da mutuwa dake tafe da takunan yaki da muggan makamai suk yiwa Baga diran mikiya

Garin Baga dake jihar Borno an sanshi a matsayin garin masunta a duk fadin arewacin Najeriya.

Da shigan 'yan ina da mutuwa cikin garin sai suka afkawa barikin soji na taron kasashen kewayen tafkin Chadi. Sun sha yin barin wuta kana suka fatattaki sojojin daga barikinsu kamar almara duk da kokarin turjewa da sojojin suka yi. Wasu sun ce an ga gawarwakin sojoji akalla goma sha daya. Fararen hula da suka halaka a cikin gari an ce suna da yawan gaske.

Majiyoyi masu tushe, ganao da wadnda abun ya rutsa dasu sun bayyana yadda maharan suka kai hare-hare kan gine-gine tare da bankawa wasu daga cikinsu wuta. Sun yi kaca-kaca da garin kuma sun yamutsashi jina-jina ya zama gandun baraguzai da tarkace. Duk mai rai yayi ta kansa. Wasu suka shiga daji wasu kuma suka soma gudu da motoci da babura. Wasu sun tsere cikin kwale-kwale kana wasu tuni suka shiga kasashen ketare da suka yi iyaka da tafkin.

Da yake lamarin ya shafi wasu kasashe, Farfasa Bube Na Maiwa na Jami'ar Diof a kasar Senegal mai sharhi akan alamuran tsaro na kasa da kasa da kuma zamantakewa yace idan yaki ne mutanen a surke suke cikin mutane sabili da haka ba'a iya tantancesu. Yanayin da ya kawo irin harin da aka kai Baga ke nan.

Farfasa Bube ya bada shawarar a koma yadda ake yi a gargariyance. Kowane mai unguwa ya san mutanensa.

Amma yace akwai babban zargin da kasashen Nijar da Chadi suke yiwa Najeriya. Sun kai nasu sojojin a sansanin dake Baga amma Najeriya bata bada adadin sojojin da suka kamata su zauna a wurin ba. Dalili ke nan da su kasashen suka janye sojojinsu. Farfasa Bube yace ba'a san dalilin da ya sa Najeriya tana dari-dari da turo jiragen yaki da aka santa dasu da kwararrun sojoji da suke zaune kara zube.

Ta sha'anin tsaro Janaral Saleh Maina mai ritaya yace lokacin Shugaba 'Yar'addua da ya bayar da umurni a yaki maharan nan da nan aka gama dasu. Duk lokacin da aka yaki wasu to idan an kammala sai an sake zama a yi nazari akan abun da aka koya da kurakuren da aka yi. A shekarar 2009 da aka yi rin wannan yakin ba'a zauna an yi nazari ba.

Kungiyoyi masu zaman kansu suna ganin abun dake faruwa ya wuce misali. Lokaci yayi da za'a hakura da juna a ji tsoron Allah da tausayin jama'a a zauna teburin shawara a yi sulhu.

Zabe ya karato amma akwai kananan hukumomi da yawa da suke hannun 'yan Boko Haram a jihohin Yobe, Adamawa da Borno. Idan ba'a kwatosu ba yanzu, da wuya a kwatosu bayan an gama zabe.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:11 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG