Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoton Binciken Mueller Bai Tabbatar Da Ko An Karya Doka Ba


Mai bincike na musamman Robert Mueller ya yi bincike game da lokuta 11 wanda ya ke kyautata zato cewa Shugaba Donald Trump ya karya doka a kokarin dakatar da bincikensa.

Binciken akan ko Rasha tayi katsalandan a zaben shekarar 2016, wanda ya lashe zaben, amma a karshe bai iya tabbatar da cewa shugaba Trump ya karya doka ba.

Rahotan mai shafi 448 da aka fitar a jiya Alhamis, ya tabbatar da cewa babu wata shaida cewa Trump ko masu yakin neman zaben sa, sun hada hannu da Rasha don yin shishshigi, a madadin shugaban kasa a zaben shekarar 2016, da nufin kada ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.

Duk da yake binciken ya rubuta mahimmancin dangantaka tsakanin mutane da gwamnatin Rasha da kuma masu yakin neman zaben sa, "shaidar ba ta isa a tabbatar da anyi laifi ba," in ji Mueller.

Amma Duk da haka, rahoto ya nuna kokarin da dama da Trump ya yi na wajen kawo cikas a binciken na zargin ko Rasha tayi katsalandan a yakin neman zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG