Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Fadakarwa Kan Illolin Miyagun Kwayoyi


Shan Miyagun Kwayoyi: Wani Yaro Na Shakar Gam Don Maye
Shan Miyagun Kwayoyi: Wani Yaro Na Shakar Gam Don Maye

Ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara rana ce na fadakar da jama’a game da illar shan muggan kwayoyi a tsakanin al’umma.

Shi dai wannan rana ya samo asali ne bayan wani zama da aka yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya a watan Disambar shekarar 1987. Inda kuma baki ya zo daya na tsayar da ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara domin bikin wannan rana na fadakar da jama’a game da illar shan muggan kwayoyi a tsakanin al’umma.

Taken bikin na bana dai shine: A saurara tukunna– Wato jin ta bakin matasa, shine matakin farko na sanin matsalolinsu domin ganin an kyautata rayuwarsu.

Matsalar shan muggan kwayoyi na daya daga cikin matsalolin da yasa gwamnatin Najeriya ta kafa dokar hana sha da sarrafa muggan sinadarin kodin (Codeine), mai saka maye a tsakanin matasa.

Ko wane mataki hukumomi daban-daban na gwamnati ke dauka domin magance wannan matsalar?

Peter Iliya, mataimakin darakta yada labarai a Hukumar Likitocin magunguna ta kasa, ya bayyana cewa, wannan matsala ce da ta addabi gwamnatin Najeriya ganin yadda matasa musamman a Arewacin Najeriya ke kwankwadar magungunan tari domin maye.

“Sabode haka dole mu tashi tsaye wajen saka dokoki masu zafi da zai magance wannan matsalar, shi yasa kake ganin a wasu kasashen irin su china ko koriya ake yanke hukuncin kisa akan duk wanda aka samu da wannan laifi na sha ko safara muggan kwayoyi,”inji shi.

To ko wane mataki Hukumar NAFDAC da hakkin kula da kuma hana shan kwayoyi ya rataya akanta ke dauka wajen magance wannan matsalar?

Dakta Musa Umar, darakta a hukumar ta NAFDAC, ya ce hukumar ta maida irin wadannan magunguna su zama wadanda sai likita ya baka izini kafin a sayar maka da shi a shagon magunguna.

“Sai dai kasan matsalar kasar nan, ba bin doka ake yi ba, don haka mutane basa bin doka. Kuma wannan magani bai da wuyan hadawa, ruwa ne da sukari da kuma sinadarin ake hadawa, don haka mutane za su same shi da araha su sha don su manta da matsalolinsu, “ inji shi.

Sannan ya bayyana cewa hukumar ta kafa dokar hana shigowa da sinadiran hadashi a kasuwa sai da izini shi ma.

Shugaban kungiyar likitocin magunguna na kasa, Ahmed Ibrahim Yakasai ya bayyana jin dadinsa game da matakin gwamnati.

“Na ji matukar dadi da wannan doka na hana shigowa da sarrafa magungunan tari, domin hakan zai taimaka wajen kare yaranmu daga shaye-shayen muggan kwayoyi, sai dai kuma akwai bukatar samar da wani tsari na farfado da wadanda suka yi nisa a shaye shayen, domin kula da su kamar yadda ya ke a wasu kasashen na duniya,” inji shi.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko wannan mataki zai taimaka wajen kawo karshen shaye-shayen muggan kwayoyi da ma kananan a Najeriya.

Saurari rohoton Babangida Jibril

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG