Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hedkwatar Tsaron Najeriya Ta Tura Dakaru Na Musamman Zuwa Filato


Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Birgediya Janar John Agim
Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Birgediya Janar John Agim

Hedkwatar tsaron Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa jihar Filato domin hada karfi da karfe da rundunar Operation Safe Heaven don tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron Bigediya Janaral John Agim ya sanyawa hannu, ta ce Babban Hafsan Tsaron Kasar Janaral Abayomi Gabriel Olonishakin ya nuna bacin ransa bisa kashe kashen rashin hankali da ake yi a jihar, ya na mai cewa sojoji baza su sa ido su bari ana irin wannan aika aika ba.

Janaral Olonishakin wanda ya ba da umarnin aikewa da karin runduna ta musamman zuwa jihar ta Filato nan take, ya ce dakarun zasu karrade dukkan yankunan da ake wannan fitina da zummar dakatar da masu aika aikar daga ci gaba da tafka ta'asar.

Shima Babban Hafsan Hafsoshin sojojin saman Kasar Air Marshall Sadique Baba Abubakar ya bada umarnin aikewa da jiragen soja masu saukar ungulu zuwa jihar Filato don taimakawa sojojin kasa wurin kwantar da fitinar.

Air Marshall Sadique Abubakar kazalika ya kuma bada umarnin tura karin kuramen jirage marasa matuka masu leken asiri don tattaro bayanai da zasu taimaka wajen kawo karshen rikicin a jihar da a baya aka santa da zaman lumana.

A halin yanzu dai shugabannin tsaron kasar na ta duba irin karin matakan da za su dauka don kawo karshen wannan rikici na jihar Filato da yaki ci yaki cinyewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG