Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Hakuri da Juna


Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Kowace ranar 16 ga watan Nuwamba ce Majalisar Duniya ta tsayar a matsayin ranar yin hakuri da juna.

A kowace shekara ranar goma sha shida ga watan Nuwamba rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe musamman domin jawo hankalin al'ummar duniya kan mahimmancin yin hakuri hakuri da juna. Manufar tsayar da ranar itace a karfafa a kuma kyautata zamantakewa tsakanin al'ummomi da addinai daban-daban.

Bisa ga shirin majalisar dinkin duniya an gudanar da taron hakuri da juna a Gombe babban birnin jihar Gomben Najeriya. Manufar taron shi ne fadakar da alumma domin nuna hakuri da jumriya da juna ko menene ma banbancen dake tsakaninsu, da fahimtar da juna da kuma inganta matsayin dan adam. Taron kuma na bayyana yadda za'a kare hakin jama'a, mutuntawa da kuma hada kan kabilu daban daban da kuma addinai daban daban.

A jihar Gombe an gudanar da irin wannan taron. Barrister Abdulhamid Ibrahim Kwamishanan shari'a na Gombe ya bada kasida a wurin taron. Ya ce majalisar dinkin duniya ta tsayar da ranar a matsayin ranar hakuri ta duniya. Hakuri kuma yana da mahimmanci a rayuwar bil adama. Ya ce yana kara tunawa mutane anfanin hakuri da kuma abun da hakuri zai haifar da kuma gudun abun da rashin hakuri zai haifar. Yana fata al'ummar Gombe sun fahinceshi a kan a dagewa a yi hakuri da juna.

Kwamishana Ibrahim ya ce akwai hanyoyi da yawa na neman haki.Akwai kotuna. Idan kana ji an taka maka haki ka je kotu ka shigar da kara. Ana iya fara shari'a daga kotu karama har a kai kotun koli na kasa. Mutane basu da hakuri ne kawai domin idan mutum ya bi fannin shari'a zai wayi gari ya ga an bashi hakinsa.

Wasu da suka halarci taron sun ce tabbas babu shakka idan an rungumi akidar zaman lafiya za'a cigaba da samun nasara domin sau da yawa duk wasu rigingimu dake faruwa jama'a suke haddasasu sanadiyar rashin hakuri.Sun ce kamata ya yi mutane su guje ma manyan 'yan siyasa masu son yin wasa da hankulan jama'a. Irin wannan taron ya kamata a yi shi a kowane gari domin hakuri nada mahimmanci wurin kawo zaman lafiya.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG