Accessibility links

Yau Ranar Lafiya ta Duniya


Ana duba yara a karamin asibiti dake kauyen Bagega a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya.

An yi kira ga gwamnatoci da ma’aikatun lafiya a Najeriya da suyi himma wajen kiwon Lafiya a Najeriya.

Shugaban sashen maguguna na asibitin koyara na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, Farfesa Balarabe Sani Garko, ya furta haka ne a wata hira da yayi da sashen Hausa ta tayar tarho domin bikin ranar lafiya ta duniya.

Yace “ranar lafiya ta duniya rana ce wace ya kamata watakila a sami wani yanayin matsala ta rayuwa ko ta lafiya a fuskaceta saboda a wayar da kai ko kuma ayi wani yunkuri daga bangaren gwamnati wanda zai taimakin mutane.”

Ya kara da cewa "Afirka dama muna da matsaloli kama, daga cututtuka wanda bai kamata ma ace suna nan ba. Yanzu misali su zazzabin cizon sauro, su zawo da amai sannan kuma ga wannan zazzabin na Ebola, wato zazzabi mai zub da jini.

Kwayar cuta da ebola virus take kawowa, sabada haka wannan rana sai dai kawai ayi jimmamin watakila rashin yin abun a zo, a gani kan abubuwan dake addabarmu.

Farfesa Garko ya kara da cewa barkewar annoba na bukatar yunkuri na gaggawa, wanda yace yakamata a kasance a shirye a kowani lokaci.

XS
SM
MD
LG