Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Tunawa Da Nelson Mandela a Fadin Duniya


Nelson Mandela

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 18 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da Nelson Mandela, shugaban Afirka ta Kudu kuma wanda yayi rajin neman ‘yancin bakaken fata.

Marigayi Nelson Mandela, ya zamanto bakar fata na farko da fara zama shugaban Afirka ta Kudu, wanda kuma yau 18 ga watan Yuli ne Mandela ke cika shekaru 100 da haihuwarsa.

A lokacin bukukuwan na bana an fara gudanar da tarurruka tun daga MDD zuwa kasashen duniya daban-daban. A sakonsa domin bikin na bana babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana cewa Mandela jan gwarzo ne mai fafutukar samun ‘yanci da kuma daidaito tsakanin al’umma, wanda kuma duniya za ta ci gaba da koyi da halayensa na kwarari domin zama abin alfahari da aiki da shi nan gaba.

Marigayi Nelson Mandela shine bakar fata na farko da ya fara zama shugaban kasar Afirka ta Kudu, bayan shafe shekaru 27 yana daure gidan Yari akan gwagwarmaya da yayi domin kawo karshen wariyar launin fata a kasar.

Mandela ya samu nasara a zaben shugaban kasa da ya tsaya takara bayan fitowarsa daga gidan Yari, yana da shekaru 77, ya kuma sauka daga shugabanci yana dan shekaru 82.

Gudaunmawar da ya bayar sakamakon jajircewarsa da kuma kyawawan manufofinsa, ya sa MDD ta karrama shi ta mayar da ranar haihuwarsa ranar da za a rinka tunawa da ita a dukkan fadin duniya.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG