Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha da Amurka Zasu Tattauna Saboda Gudun Karo da Juna a Syria


Amurka da Rasha

Rasha ta musanta cewa, hare haren da ake kaiwa ta sama a Syria,suna shafar wadansu banda mayakan ISIS, yayinda take shirin tattauna batun ayyukan soji da Amurka da nufin guje samun sabani a kasar da yaki ya daidaita.

Ministan harkokin kasashen ketare na Rasha Sergei Lavrov ya shaidawa manema labarai a birnin New York, cewa, wadannan rahotannin basu da tushe, dangane kuma da cewa, wadansu hare haren sun shafi fararen hula, Lavrov yace bai sami wannan labarin ba.

Ya bayyana haka ne jiya Laraba bayan ganawarsa da sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry, wanda yace ma’aikatun na Amurka da na Rasha zasu tattauna nan ba da jimawa ba, mai yiwuwa yau alhamis, gudun karo da juna a Syria.

Jiya sakataren ma’aikatar harkokin tsaron Amurka Ash Carter yace mai yiwuwa ne Rasha ta kai hare haren ta sararin sama a Syria kan wadansu wurare ne da babu ‘yan kungiyar ISIS.

Wata majiyar pentagon ta shaidawa Muryar Amurka cewa, kungiyar mai tsats-tsauran ra’ayi ta yada zango ne a biranen Raqqa da Aleppo da kuma birnin Deir al-Zour. Yayinda galibin wadanda suke kokarin hambare gwamnatin shugaban kasar Syria Bashar al-Assad suke birnin Homs.

XS
SM
MD
LG