Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Musanta Janye Ma’aikatan Tsaronta Daga Venezuela


Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov

Rasha ta musanta fadawa shugaban Amurka Donald Trump za ta janye ma’aikatan tsaronta daga Venezuela.

Rasha ta musanta cewa ta fadawa shugaban Amurka Donald Trump cewa, za ta janye ma’aikatan tsaronta daga Venezuela, sanarwar da ta saba kalaman da shugaban Amurkan ya yi.

A jiya Talata Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce, "na yi mamaki da na karanta wannan labarin, mu ba mu sanar da kowa ba, watakila ya karanta labarin ne a jaridar Wall Street Journal."

Lavrov na mayar da martani ne kan wani sakon Twitter da Shugaba Trump ya wallafa a shekaranjiya Litinin

A watan Maris ne Trump ya ce, Rasha "dole ne ta fita" daga kasar ta Venezuela da ke kudancin Amurka, bayan da ta kai jirage dauke da kayayyaki da masu ba da shawara don taimakawa Shugaba Nicolas Maduro, yayin da kasar ke fama da rikicin siyasa.

Amurka dai na so ne a hambarar da shugaba Maduro, wanda suke kawance da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, yayin da dubban 'yan kasar Venezuelan suka bazama akan tituna suna zanga zangar adawa da gwamnatinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG