Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Abun Yi Ke Sa Wasu Matasa Shiga Kungiyar Boko Haram - Sabon Bincike


Taro kan mayakan Boko Haram
Taro kan mayakan Boko Haram

Akwai bukatar mahukunta su dauki matakan da suka dace, don yaki da ayyukan ta'addanci a yankin hamada, a cewar masana.

Wani sabon bincike da wasu masana suka gudanar akan rikicin mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ya gano wasu daga cikin dalilan da suka sa matasa da yawa shiga kungiyar Boko Haram.

Dr. Abba Sadik, wani sanannen dan jarida da ke birnin Paris, na daga cikin wadanda suka gudanar da binciken, ya ce sun yi nazari kan abubuwa da dama da suka ja ra’ayin matasa shiga kungiyar Boko Haram kuma sun gano cewa da yawa daga cikin su ba don addini suka shiga ba, wasu kuma sun shiga kungiyar ne bisa tunanin zasu samu arziki saboda sun dauke ta kamar wata sana'a tunda basu da abin yi.

Taron Boko Haram
Taron Boko Haram

Ya kara da cewa wasu da suka shiga kungiyar da sunan addini amma daga baya suka gane cewa kungiyar Boko Haram ba addini ta ke bi ba kuma suka so su ja da baya an kashe su.

Game da wadanda rikicin Boko Haram ya fi shafa, Dr. Sadik ya ce mafi akasari mata da yara ne suka fi jin jiki. Mata da yawa sun zama gwamraye, yara kuma sun zama marayu. Wasu mazan kuma ba su san halin da matansu ke ciki ba tun bayan da aka sace su.

Taron Boko Haram
Taron Boko Haram

A nashi bangaren Zanna Hassan Bugoma, ya na ganin cewa a kowane lokaci jama’a kan kalli ayyukan ta’addanci da ‘yan kungiyar ke kai wa ba tare da la’akari da bangaren gwamnati ba, kuma ga dukkan alamu babu niyar kawo karshen wannan yakin yanzu.

Duk da cewa shugaban kasa da jami'ansa na iya kokarin su wajen kawo karshen rikicin, akwai bukatar gwamnati ta kara daukar matakai da suka dace don kawo karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya da ma makwabtanta baki daya.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga N’Djamena a kasar Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG