Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Kudi Ya Kashe Kasuwar Raguna A Adamawa

Kasuwar ragunan layya
Kasuwar ragunan layya

Biyo bayan tashin gwauron zabi da kayayyaki suka yi a kasuwannin Nigeria ta dalilin matsalolin tattalin Arziki da ya janyo rashin kudade a hannun jama’a, mutane da dama ba za su samu damar yin layya bana ba.

Duk da cewa bana-farashin raguna sun sauka sosai idan aka kwatanta su da bara, masu sayar da raguna na fama da rashin kasuwa wanda suka danganta da rashin kudade a hannun jama’a.

Ahmadu Aliyu, wani mai sana’ar dabbobi ne a Jalingo fadar jihar Taraba, ya bayyana cewa akwai saukin dabbobi a bana, lamarin ya fi na bara idan har aka kwantanta da yadda kasuwar ke gudana, inda yace ma akwai raguna masu sauki da mutum zai iya saye gwargwadon wadatarsa.

Shi ma wani dillalin dabbobi ya danganta tsadar a yanzu da yan baranda da kuma tashe tashen hankulan da aka yi fama da shi da cewa su suka jawo tashin gwauron zabin.

To sai dai kuma, Mallam Muhammad Tukur Misa, wani magidanci ne da ya zo sayan ragon layya,yace duk da halin da ake ciki, shi kan tabarkallah.

Malam Ahmadu Gassol wani magidanci mai ya’ya biyu dake shirin hidimar sallah, ya bayyana cewa lallai akwai tsananin rashin wadatan kudade a hannayen jama’a, ga rashin biyan albashi, to amma duk da haka za su kokarta, domin samun lada.

A halin yanzu dai ma’aikata ma na kuka da rashin biyansu albashi ta yadda suke gwagwarmayan ganin sun yi hidimar sallah ko da kuwa da bashi ne in sun samu albashin su biya. Yayin da a bangare guda, ake iya ganin cincirindon jama’a a bankuna suna kokarin cire kudaden ajiyansu domin gudanar da shiye-shiryen sallah.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG