Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro Ya Sanya Ilimi A Arewa Koma Bayan Shekara 20 - Abdulsalami


Abdulsalam Abubakar Tsohon Shugaban Kasar Najeriya.
Abdulsalam Abubakar Tsohon Shugaban Kasar Najeriya.

Tsohon Shugaban kasa na mulkin soji a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana damuwa kan yadda ilimi a Arewacin kasar ya sami koma baya da akalla shekaru 20 sakamakon rashin tsaro a yankin.

Kalaman na janar Abdualami Abubakar na zuwa ne biyo bayan furucin shugaba Muhammadu Buhari na bayyana bakin cikinsa game da kisan gillar da aka yiwa wasu ‘yan kasar, ciki har da wani shugaban‘ yan banga da kuma dagacin Dabna, a wani kauye da ke garin Dugwaba, a karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.

Janar Abdulsalami ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar raya dimokradiyya da kare hakkin dan Adam karkashin jagorancin shugabanta na jihar, Kwamared Abdullahi Jabi, a gidansa da ke Minna a jihar Neja.

Tsohon shugaban na mulkin soji ya bayyana bakin ciki game da yadda dubban yara da suka kai munzalin zuwa makaranta ba sa iya zuwa makarantar sakamakon rashin tsaro, a yayin da yan bindiga ke yin garkuwa da wadanda ke zuwa makarantar don neman kudin fansa.

Haka kuma, janar Abdulsalami ya ce "Arewa na fuskantar tsananin rashin tsaro inda wasu mutane marasa kishin ke ci gaba da satar ‘ya’yan al’umma", inda kuma ya yi musu gargadin cewa "za su girbi abin da su ke shukawa" kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

A yayin mayar da martani kan kisan gillar jihar Adamawa a ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari, ya danganta lamarin da rashin imani da mutunta ran dan adam, inda ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiyuwa wajen zakulo masu aikata aika-aikar da kuma hukunta su.

An dai kwashe sama da shekaru 10 ana fama matsalar rashin tsaro a yankunan Arewa maso gabas da fama da rikicin mayakan Boko Haram, yayin da Arewa maso yamma kuma ke fama da hare-haren yan bindiga dadi da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa tare da kashe-kashen manoma.

XS
SM
MD
LG