Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Wutar Lantarki Ya Hana Jirgin Alhazai Sauka a Yola


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya ranar Litinin 14 ga watan Oktoba shekarar 2013.
Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya ranar Litinin 14 ga watan Oktoba shekarar 2013.

Jirgin dake dauke da alhazan Adamawa bai iya sauka a Yola ba domin rashin wutar lantarki lokacin da ya iso

Jirgin da ya kawo wasu alhazai dari biyar 'yan jihar Adamawa daga Saudiya bai iya sauka a Yola ba babban birnin jihar Adamawa domin rashin wutar lantarki.

Jirgin da ya fito daga Saudiya dauke da fiye da alhazai dari biyar bai iya sauka ba domin rashin wutar lantarki. Dole ya karkata kai zuwa filin saukar jirage na Malam Aminu Kano dake Kano. A can Kano aka saukar da alhazan. Inji wasu alhazan haka aka bar su ba abinci ko wurin sa kai har kusan karfe hudu na asuba kafin a basu wani abun tabawa.

Sanadiyar rashin tanada masu wurin sa kai a filin jirgin mutane fiye da dari biyar suka kwana a wajen Allah inda suka ta yin fama da sauro. Wani daya daga cikin ma'aikatan jirgin ya yi alkawarin zuwa samo masu abinci da motoci da zasu kaisu otel inda zasu kwana, amma sai ya bace.

To sai dai hukumar alhazai ta jihar Adamawa ta ce ba laifin masu jirgin ba ne domin sun cika aikinsu. Matsalar rashin wuta ta jawo kaisu Kano. Sakataren hukumar Alhaji Salihu Danjuma ya ce wannan abu ne da jihar ya kamata ta duba domin a guji na gaba.

An ce wannan ba shi ne karon farko ba da filin jrigin na Yola ya samu matsalar wutar lantarki. Jami'an filin sun ce lamarin ya fi karfinsu.

Ga Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG