Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Zaman Lafiya A Najeriya Siyasa Ce - In Ji Kungiyar Mata


Tattakin Kungiyar Mata A Jihar Kaduna
Tattakin Kungiyar Mata A Jihar Kaduna

Taron tattakin da kungiyar Eye Opener ta mata ta gudanar a jihar Kaduna ya hado mata daga addinai daban daban, inda suke kiran da a dage da yin addu'a domin neman zaman lafiya na irin halin da ake ciki a Najeriya.

Wata kungiyar mata mai suna “Eye Opener” a turance ta ce rashin zaman lafiya da ke damun Najeriya siyasa ce.

Kungiyar, wadda ta yi tattaki a cikin garin Kaduna don nuna bukatar zaman lafiya na halin da ake ciki, ta ce akwai bukatar mutane su dage da yin addu'a.

A lokacin da shugabar kungiyar, Madam Magret Julius, ta kewa manema labarai karin bayani ta ce irin halin da ake ciki yanzu addu’a ce kawai mafita.

Shima jami’in ‘yan sandan da ya wakilci kwamishin ‘yan sanda jihar Kaduna, CSP Uzairu Abdullahi, ya ce irin wannan taro zai taimaka wajan tabbatar da zaman lafiya mai daurewa a Najeriya.

CSP Abdullahi ya kuma kara da cewa zaman lafiya hakki ne akan kowa ba na jami'an tsaro kadai ne ba.

Wasu mahalarta wannan tattakin zaman lafiya sun nuna damuwar su ganin yadda zamantakewa ta tabarbare yanzu, inda su ka buga misalai da yadda kiristoci da musulmai ke cudanya da juna a shekarun baya.

Taron tattakin zaman lafiyan da matan suka shirya dai sharar fage ne na ranar zaman lafiya ta duniya da Majalissar Dinkin Duniya ta ware ranar 21 ga watan satumbar Kowacce shekara da nufin nuna bukatar zaman lafiya a ko ina.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00



Facebook Forum

XS
SM
MD
LG