Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rex Tillerson ya Isa Gabas ta Tsakiya a Yau Jumma’a


Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Amurka
Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya isa Gabas ta Tsakiya a yau Jumma’a domin halartar taron tattaunawa tsakanin gwamnatin Saudiya da ta Iraqi, da kuma duba hanyoyin da za’a karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shirin zaman tattaunawar yazo ne dai dai lokacin da dangantaka tsakanin Riyadh da Baghdad ta fara armashi. Ana kallon haduwar tasu a matsayin wani yunkuri na Amurka wajen rage karfin sa hannun Iran a Iraqi ta hanyar karawa Baghdad karfin gwiwa ta zama kawa ta kusa ga Riyadh.

Mai magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ta ce Amurka na murna da dangantakar dake tsakanin Iraqi da Saudiya inda ta bada misali da yadda aka bude kan iyaka a tsakanin kasashen biyu wajen shigar da kaya.

Za’ayi zaman ne a Riyadh babban Birnin Saudiya, bayan watanni hudu da kasashen biyu suka rattaba hannu akan yarjejeniyar karfafa alaka tsakaninsu da suke makwabtaka da juna, a wani yunkuri na rage ikon fada a ji da Iran ke dashi a yankin.

A cewar ma’aikatar harkokin wajen ta Amurka, a yayin da Tillerson ke Riyadh, zai gana da Shugabnnin Saudiya daban daban domin tattaunawa kan rikicin Yemen da kuma rikicin da ake ciki a yanzu akan mashigin tekun Gulf, da Iran da kuma wasu muhimman al’amura da suka shafi kasashen biyu a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG