Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikakken Mai Satar Mutanen Nan Ya Sake Shiga Hannun Hukuma


Gagararren Mai Satar Mutanen Nan, Wadume

Biyo bayan sake cafke jagoran gungun masu satar mutanen nan na jihar Taraba a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano, bayan da tun da farko sojoji suka bude wa ‘yan sandan IRT wuta a jihar Taraba suka hallaka jami’an ‘yan sandan uku da suka kamo dan ta'addan suka kuma sake shi ya kama gabansa.

Yanzu haka masana da kwararru a Najeriya sun yaba wa ‘yan sanda a kan namijin kokari da suka yi wurin zakulo mutumin, suna cewa wannan na nuna lalle fa ‘yan sandan Najeriya jajirtatttu ne.

Masanin Halayyar bil'adama da harkar tsaro, Farfesa Mohammed Tukur Baba ya ce wannan na nuna irin sabon babi da ‘yan sandan suka bude a sha'anin tsaro, duba da irin bajintar da suke ta nunawa da ba ayi tsammani ba, a don haka matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta ba wai ya gagari ‘yan sanda ba ne.

Farfesa Baba ya kara da cewa matakai da suke bi su kamo irin wadannan manyan yan ta'adda ya nuna cewa in sun dukufa kuma suka samu goyon bayan jama'a to fa lalle ‘yan sandan zasu magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Kamo irin wannan babban dan ta'addan inji masanin ka iya aikewa da sako ga duk masu son tafka aika aika, don hakan ya fara bada tsoro cewa lalle komai nisan jifa kasa zai fado, don kuwa dan sandan Najeriya ba kanwan lasa bane.

Lauyan nan mai fafutuka Barrister Yakubu Sale Bawa yace shi tuni yana da kwarin gwiwar lalle ‘yan sandan zasu sake cafke shi Wadumen, duba da cewar lalle ‘yan sandan Najeriya in zasu yi aiki zasu yi, kuma cafke wannan Wadumen zai fito da dalla dallan me ya faru.

Ga dai rahoton wakilinmu Hassan Maina Kaina daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3-1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG