Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Bayan Zabe Ya Janyo Asarar Rayuka A Taraba


TARABA: Gwamnan Jihar Taraba Arch Dickson Isyaku
TARABA: Gwamnan Jihar Taraba Arch Dickson Isyaku

An baza jami'an tsaro da suka hada da sojoji a Jalingo fadar jihar Taraba domin maido da doka da oda, bayanda rikicin bayan zabe ya janyo asarar rayuka.

Rikicin na Jalingo, ya taso ne lokacin da hatsaniya ta kaure a tsakanin wasu matasa dake murnar nasarar da gwamnan jihar akitet Darius Dickson Isiyaku na jam'iyar PDP ya samu,yayin da wasu matasan kuma suka ce ba zata sabu ba,lamarin da yakai kone kone da kuma asarar rayuka a cikin garin Jalingo.

Baya ga Jalingo fadar jihar rahotani na cewa, wasu masu bukukuwan kan tare matafiya akan hanyar Wukari suna kwace musu dukiya,kamar yadda wasu da suka sha da kyar suka tabbatarwa Sashen Hausa.

Kawo yanzu rundunan yan sandan jihar ta tabbatar da abubuwan dake faruwa inda ta yi gargadi na hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan tashe tashen hankulan.

Gwamnatin jihar dai bata maida martani ba tukunna, amma wannan na zuwa ne yayin da tun a jiya litinin ta kafa dokar hana fita daga large shida na maraice zuwa shida na safe.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul'ziz.

Rikicin zabe ya janyo asarar rayuka a Taraba-3:50"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG