A sanarwar da hukumomin mulkin sojan kasar suka fitar sun kudiri aniyar yin anfani da matakan da suka dace domin kubutar da jami’an kasar da gwamnatin Benin ta kama bisa zargin shiga kasarta ba bisa ka’ida ba.
Sai dai ana samun sabanin ra'ayoyi kan yadda hukumomin sojin Nijar ke tunkarar rikici tsakaninta da makwabciyarta.
Yayinda wasu ke ganin abi hanyar lalama wajen magance wannan rikici, wasu kuma na goyawa mahukuntan Nijar baya inda suke ganin hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar su bi hanyoyin da suka da ce domin kawo karshen wannan takaddama.
A hankali dangantaka tsakanin hukumomin Benin da na Nijar na kara tsami inda bakaken maganganu ke cigaba da fitowa a bakunan shuwagabannin kasashen da magoya bayan su.
Wasu kungiyoyin farar hula a Nijar na ganin akwai bukatar kungiyoyin duniya su shiga cikin lamarin Nijar da Benin domin warware rikicin kasashen biyun cikin ruwan sanyi.
Sai dai al’ummomin kasashen biyu sun tunatar da shuwagabannin kasashen dangantakar dake tsakanin kasashen biyu mai dimbin tarihi tare da yin kira da a samar da sulhu a tsakanin su.
Saurari rahoton Hamid Mahmoud:
Dandalin Mu Tattauna