Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Boko Haram Ya Lankwame Rayukan Mutum Dubu 11 Inji Wani Nazari


Irin hare-haren 'yan boko haram masu hallaka mutane a arewa maso gabashin Najeriya.

Sashen Nazarin Al’amurran Yau da Kullum na Duniya a Jami’ar John Hopkins ta nan Amurka ne ya gabatar da rahoton.

Wani sabon rahoton da ya fito yace a lalace mutanen da aka hallaka a sanadin ta’asar ‘yan Boko Haram a sashen arewa-maso-gabashin Nigeria sun kai mutane dubu goma sha daya.

Wadanan alkalumman sun bayyana ne a cikin wani nazarin da Sashen Nazarin Al’amurran Yau da Kullum na Duniya a Jami’ar John Hopkins ta nan Amurka ta gudanar bayanda ta hada hancin jimillar yawan mutanen dake rasa rayukkansu tun daga lokacinda aka faro wannan tashin hankalin a shekarar 1998.

A cikin wannan kasidar da aka wallafa a cikin jaridar Washington Post, masu nazarin sunce yau a duniyar nan, ba wata tarzoma da kai ta Boko Haram ta fuskar asarar rayukkan mutane da ake. Kasidar tace ko a cikin shekara daya kawai, daga watan Yulin 2013 da watan Yunin wannan shekarar da muke ciki, mutanen da aka kashe a tarzomar Boko Haram din tafi mutane 7,000, har ta nuna cewa ko ka hada hancin yawan mutanen da ake kashewa a yake-yaken Iraq da Afghanistan, ba zasu kai yawan wadanda ke hallaka a hannun ‘yan Boko Haram da ma’aikatan tsaron Nigeria ba, wadanda suma rahoton yace ana zarginsu da yiwa dimbin mutane kisan gilla a kokarin da suke na jan daga da ‘yan Boko Haram din.

Rahoton yace in aka hada hancin dukkan mutanen Nigeria da suka rasa rayukkansu a tashe-tashen hankulla masu alaka da addini, kabilanci, siyasa da tattallin arziki da suka faru daga 1998 zuwa yau, za’a ga cewa sun fi dubu talatin.

XS
SM
MD
LG