Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kan Iyaka Yayi Sanadiyar Jikata Mutane 20 da Asarar Dukiyoyi a Jihar Neja


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.

Rikicin kan iyaka da ya barke a garin Gulu cikin karamar hukumar Lapai a jihar Neja ya lafa.

An yi tashin hankalin da ya yi sanadiyar jikata mutane 20 tare da kona kasuwa da kaddarori a garin Gulu cikin jihar Neja. Shaguna da dama aka kone a cikin garin.

Bayyanai sun tabbatar da cewa rikicin iyaka ne ya kawo tashin hankalin tsakanin Gulu ta arewa da kuma Gulu ta yamma.

Alhaji Muhammed Sani dagacin garin Gulu ta arewa yayi karin haske akan asarar da aka samu lokacin tashin hankalin. Yace kodayake ba'a yi asarar rai ba amma wadanda suka jikata zasu kai ashirin ko talatin. An kone shaguna da gidaje da dama.

Tuni mahukuntan jihar Neja suka ce sun dauki matakan shawo kan matsalar kamar yadda Dr. Isa Yahaya Batsa kwamishanan ma'akatar dake kula da harkokin dabbobi wanda kuma ya fito daga yankin yace. Inji shi ana nan ana yin taro domin a lalubo bakin zaren warware matsalar.

Rundunar 'yansandan jihar ita ma ta tabbatar da aukuwar rikicin. Tace ta tura karin jami'an tsaro a yankin domin dawo da doka da oda.

Ga rahoton Mutapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG