Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rodrigo Duterte Ya Yi Na'am Da Batun Hakkin Bil-Adam: Justin Trudeau


 Justin Trudeau da Rodrigo Duterte
Justin Trudeau da Rodrigo Duterte

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce “kama daga tsakiyar shekarar 2016, jami’an tsaro da kuma wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun kashe mutane dubu 7 da ake zargin cewa masu shan kwaya ne ko masu sayar da ita.

Firayim minista Justin Trudeau na kasar Canada ya ce yayi magana kan batun hakkin bil Adama tare da shugaba Rodrigo Duterte na Philippines, wanda dubban mutane suka mutu a sanadin irin matakan da yake dauka na murkushe safara da shan miyagun kwayoyi.

Trudeau ya fadawa ‘yan jarida yau talata a Manila cewa ya "jaddada ma" Duterte bukatar mutunta doka da kuma hakkin bil Adama," a tattaunawar da suka yi a gefen taron kolin kungiyar kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya, ASEAN, a babban birnin na Philippines. Yace, “shugaban na Philippines ya karbi kalamu na sosai a tattaunawar da muka yi cikin raha da abota.”

Matakan da shugaba Duterte ya dauka na murkushe safarar muggan kwayoyi da shan su, jim kadan da hawarsa kan mulki a shekarar da ta shige, sun yi muni suka haddasa zubar da jini. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce “kama daga tsakiyar shekarar 2016, jami’an tsaro da kuma wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun kashe mutane dubu 7 da ake zargin cewa masu shan kwaya ne ko masu sayar da ita.

Cikin wannan adadi ‘Yan sanda sune kashe mutane dubu 3 da Dari Daya da Goma Sha Shida.” Shugaba Donald Trump na Amurka bai tabo batun keta hakkin bil Adama da ake zargin Duterter da aikatawa ba a tattaunawar da suka yi jiya litinin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG